Beenharun Autofix

Salam sunana engineer
Ibrahim haruna director na beenharun autofix Dake Abuja a Nigeria


Barka da zuwa tashar gyaran mota!

Tare da fiye da shekaru 12 na kwarewa a gyaran motoci, ina nan domin sauƙaƙa muku gano matsalolin mota. Bidiyoyina suna bayani dalla-dalla akan kowace irin matsala ta mota, daga matsalolin injin zuwa na electrician dana kafa harda body works.

Me zaka samu a wannan tasha?
✅ Jagoranci mai sauƙi akan gano matsalolin mota
✅ Yadda zaka gyara motarka da kanka
✅ Shawarwari daga ƙwararre don ceton kuɗi da lokaci
✅ Sabbin bayanai akan gyaran mota da kiyayewa

Ina mai da hankali wajen ba ku bayani a bayyane kuma mai inganci, domin ku iya gyaran motarku da kanku cikin kwarin gwiwa. Burina shine taimaka muku ku adana lokaci da kuɗi yayin da kuke kula da motarku cikin koshin lafiya.

Kar ka manta ka yi subscribe don samun sabbin bidiyoyi da bayanai masu amfani!

Muna gyaran ko wacce irin mota