Sirrin Fatahi

Sirrin Fatahi – Mawakin Musulinci ﷺ
Assalamu Alaikum. Ni ne Abdullahi Auwal Umar, wanda aka fi sani da Sirrin Fatahi, mawakin yabon Manzon Allah (SAW) tun daga shekarar 2010. Asalina daga Charanchi LGA, Jihar Katsina, amma ina zaune a Gwale, Kano.
Wakokina sun samo asali ne daga ƙaunar Musulunci da Musulmai, inda nake amfani da fasaha da ilimi wajen isar da sakon yabo da faɗakarwa. Daga cikin shahararrun wakokina akwai:

- Sirrin Fatahi
- Annabi Yafi Nan
- Ahmadul Wara
- Labbaikum Shehu
- Ruhul Arifina

Ina ƙaunar karatu da neman ilimi, kuma ina amfani da wakokina wajen karfafa iman, ilmantarwa da ƙarfafa soyayya ga Annabi Muhammad (SAW) da waliyyai masu gaskiya.
Ku yi subscribe don jin wakokin yabo masu ɗauke da hikima, natsuwa da soyayyar Annabi (SAW).