Na Wushishi TV

Shirin "Mahangar Tsaro da Zaman Lafiya" zai dunga zuwa a YouTube channel namu mai suna Na Wushishi TV.

Shiri ne da zai dunga kasancewa da mutane daban-daban da su ka ha'da da Jami'an Tsaro, 'Yan Siyasa, Sarakunan Gargajiya, Malaman Addini, 'Yan Kasuwa, Ma'aikatan Gwamnati da makamantan su, domin tattaunawa da su akan al'amurar da su ka shafi harkar tsaro da kuma zaman lafiya a sassa daban-daban na 'kasar Nigeria.

Domin 'karin bayani ko kuma sha'awar kasancewa a cikin shirin sai a tuntu'bi jagoran shirin Kabir Wushishi a lambobin waya kamar haka: MTN 08035975698 ko kuma GLO 08056631578.