Ranar Wanka TV

Ranar wanka shiri ne da ke dauke da bayanai da suka Shafi al'amuran Yau da kullum na rayuwar al'umma, kuma yake yin fashin baki da warware zare da abawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi arewacin Najeriya wadanda suka hada da gwamnati, siyasa, kiwon Lafiya, sufuri, al'adu, kimiya da fasaha, wasanni da dai sauransu. Wannan shirin ya samu karbuwa a duk fadin kasar nan domin irin gudunmuwar da yake bayarwa wajen yin tasiri ga rayuwar 'yan arewacin Nijeriya. Wannan shirin na Ranar Wanka zai baku dama domin tofa albarkacin bakinku a dandalinmu na yanar gizo. Wannan shafin shine Shafi na sahihi da ke dauke da sunan shirin ranar wanka Wanda ALHAJI ALTINE SHEHU KAJIJI ya kirkira domin jin ra'ayin masu kallon shirin