Bello Yabo ya lashi takwabin cewa ba zai taɓa yafe wa Buhari ba!
Автор: Madubi TV
Загружено: 2025-07-14
Просмотров: 14319
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, fitaccen malamin addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya, Sheikh Bello Yabo, ya bayyana cewa bai yafe wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba – kuma ba zai taɓa yi ba. A cewarsa, irin halin da talakawa suka shiga a lokacin mulkin Buhari ya bar mummunan tabo a zuciyar sa. Wannan kalami ya tada kura sosai tsakanin magoya baya da masu adawa da gwamnatin da ta gabata.
Me ya sa Bello Yabo ya ɗauki wannan matsayi? Me ya faru tsakanin sa da gwamnatin Buhari? Ku kalli wannan bidiyo domin jin cikakken bayani da martanin jama'a.
#BelloYabo #Buhari #Arewa #YafeWaBuhari #HausaNews #MadubiTV
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео mp4
-
Информация по загрузке: