Ministan Tsaro Muhammed Badaru Abubakar yayi murabun a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ta'azzara
Автор: FVM Hausa International Falala TV
Загружено: 2025-12-01
Просмотров: 49
Yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka jefa ƙasar cikin mawuyacin hali, Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ajiye mukaminsa.
A cikin wasikar murabus da ya rubuta a ranar 1 ga Disamba, 2025, Badaru ya bayyana dalilan lafiya a matsayin abin da ya tilasta masa yin murabus. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa.
Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro domin shawo kan matsalolin da suka addabi ƙasar. Wannan lamari ya jawo cece-kuce a fagen siyasa da tsaro, inda ake ganin sauye-sauye za su iya faruwa a shugabancin tsaro na ƙasa.
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео mp4
-
Информация по загрузке: