Популярное

Музыка Кино и Анимация Автомобили Животные Спорт Путешествия Игры Юмор

Интересные видео

2025 Сериалы Трейлеры Новости Как сделать Видеоуроки Diy своими руками

Топ запросов

смотреть а4 schoolboy runaway турецкий сериал смотреть мультфильмы эдисон
dTub
Скачать

Ku san Malamanku: Sheikh Sharif Ibrahim Saleh SHIRIN BBC HAUSA

Автор: الشيخ ابراهيم صالح الحسيني Sheikh Ibrahim Saleh

Загружено: 2020-10-23

Просмотров: 25592

Описание:

Shirin ya fara ne da Sheik Sharif Ibrahim Saleh, wanda ya yi karatu a wurare da dama da suka haɗa da Makka da Madina da Masar da Pakistan da sauran su, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Ƙur'anin nan Mahmud Khalilul Khusari a Masar.

Sheikh Shariff Saleh shi ne shugaban kwamitin fatawa ta addinin musulunci a Najeriya.

Sheik Sharif ya ce ya fi sha'awar ɓangaren ilimin Ƙur'ani da Hadisi kuma a nan ne ya fi ƙwarewa. Sannan ya haddace Hadisan da suke cikin Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai.

Malamin dai ɗan ƙabilar Shuwa Arab ne, sannan ya ce ya fi son abinci mara yaji.

A cikin hirar, Sheikh ya ce ya kamata malamai su daina hauragiya da zage-zagen juna. "Kamata ya yi su haɗa kai wajen ilimantar da mutane.''

Sannan ya koka kan yadda ya ce ake siyasa a Najeriya ba don ci gaban al'umma ba.

'Yadda za a magance matsalar mabarata'
Ganduje zai sanya hannu a takardar kashe wanda ya yi ɓatanci ga Annabi
line
Wane ne Sheik Sharif Ibrahim Saleh?
An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh a ranar Asabar, 12 ga watan Mayun 1938 a garin Aredibe, da ke kusa da Dikwa ta Jihar Borno.

Mahaifinsa, shi ne Sheik Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawwy, wanda wani babban malami ne da ya yi fice a fagen ilimin addinin Musulunci.

Sheik Ibrahim Saleh ya fara koyon Al-Ƙur'ani mai girma tun yana ɗan ƙaramin yaro, inda a kullum yake tare da mahaifinsa da dare wanda kullum aikinsa shi ne yin nafila cikin dare.

Wannan ne ya sa Malamin ya fara haddace ayoyin Ƙur'ani tun kafin ya shiga makaranta gadan-gadan. Sau da dama ɗaliban da ke karatu a wurin mahaifinsa na yawan mamakin Ibrahim kan irin ƙoƙarinsa da basirarsa sakamakon yadda yake cin su gyara a karatu duk da sun sha gabansa.

Daga shekarun 1944 zuwa 1964 ne malamin ya matsa ƙaimi wajen haddace Ƙur'ani da koyon wasu litattafai da darusa.

Ya kuma fara neman ilimin Ƙur'ani ne tun a cikin gidansu, wanda daga baya ya koma sauran tsangayu inda ya je wurare kamar Tarmuwa da Gulumba da Gide da Maishumari da Maiduguri.

Akwai manyan malamai da dama da suka yaba da ƙoƙarin Sheik Ibrahim Saleh tun yana ƙarami kamar irin su Sheik Ahmad Muhammadul Habib, wanda jika ne ga Sheik Al-Tijani, akwai kuma Sheik Muhammad Mustapha Alawi da Sheik Tijjani Usman da dai sauransu.

Sheik Ibrahim Saleh ya shafe shekara 20 yana neman ilimi a matsayinsa na ɗalibi, kuma ya koyi kusan dukkan karatunsa a Najeriya, amma ba hakan ke nufin duka malamansa ƴan Najeriya ba ne.

Karatun Sheik Ibrahim ya fi ƙarfi a ɓangaren Hadisi da Usulul Fiƙihu da Ilmun Kalam da kuma Tafisiri. Misali, duk wata aya daga cikin Ƙur'ani idan aka ambato ta, malamin zai iya faɗin idan tana da alaƙa da wani hadisi a tattare da ita. Malamin ya kuma yi nisa ƙwarai a karatun Tauhidi da Fiƙihu.

Sheik Ibrahim ya yi aiki da gwamnatoci daban-daban tun daga 1976 musamman gwamnatin tarayya.

line
Mai ba da shawara
Ana yawan saka shi a duk wani kwamitin addinin Musulunci da zai bayar da shawara kan wasu tsare-tsare da gwamnati ke son ɓullowa da su da ke suke da muhimmanci ga addini ko kuma waɗanda za su iya jawo matsala.

Ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin ƙasar ke yawan tura wa zuwa ƙasashe a matsayin wakilan gwamnati ko kuma cikin wata tawaga zuwa ƙasashe kamar Saudiyya da Iran da Masar da Turkiyya da Libiya da Moroko da dai sauransu.

Sheik Ibrahim Saleh ya rubuta sama da litattafai 400 ya kuma gabatar da ƙasidu sama da 100 duka a harshen Larabci.

Ku san Malamanku: Sheikh Sharif Ibrahim Saleh SHIRIN BBC HAUSA

Поделиться в:

Доступные форматы для скачивания:

Скачать видео mp4

  • Информация по загрузке:

Скачать аудио mp3

Похожие видео

Fahimtar Da Ta Tsarkake Allah Daga Siffofin Halittu الرَّحْمَٰنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى

Fahimtar Da Ta Tsarkake Allah Daga Siffofin Halittu الرَّحْمَٰنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى

JAWABI AKAN MAULIDI DAGA SHEIKH IBRAHIM SALEH 2013

JAWABI AKAN MAULIDI DAGA SHEIKH IBRAHIM SALEH 2013

Асвад - Хьикматци а, хазчу хьехьахамци Делан дине нах кхайкхар

Асвад - Хьикматци а, хазчу хьехьахамци Делан дине нах кхайкхар

Фронт-2026. Оставь надежду?

Фронт-2026. Оставь надежду?

ME AKE NUFI DA TARBIYYA A DARIKAR TIJJANIYYA DA HAKIKA A MUSULUNCI

ME AKE NUFI DA TARBIYYA A DARIKAR TIJJANIYYA DA HAKIKA A MUSULUNCI

ЧТО ПИТЬ, Чтобы Быстро Улучшить Кровообращение В Ногах? После 60! Доктор Мясников

ЧТО ПИТЬ, Чтобы Быстро Улучшить Кровообращение В Ногах? После 60! Доктор Мясников

TOFAH: MAL KABIRU KIFI YA KUNYATA IZALA, SAURARI YANDA DR SHATTIMA ALMISKIN YAYI RAGA-RAGA DASHI.

TOFAH: MAL KABIRU KIFI YA KUNYATA IZALA, SAURARI YANDA DR SHATTIMA ALMISKIN YAYI RAGA-RAGA DASHI.

Индийские мигранты заполнили Россию и Прямая линия с больным Кадыровым | Голосовой чат NIYSO

Индийские мигранты заполнили Россию и Прямая линия с больным Кадыровым | Голосовой чат NIYSO

Hikimar Musulunci (Alamomin Mutuwa) sheikh ibrahim saleh

Hikimar Musulunci (Alamomin Mutuwa) sheikh ibrahim saleh

سورة البقرة (كاملة) للشيخ محمد الفقيه لحفظ وتحصين المنزل وجلب الرزق البركة تلاوة رائعة Sourah Baqara

سورة البقرة (كاملة) للشيخ محمد الفقيه لحفظ وتحصين المنزل وجلب الرزق البركة تلاوة رائعة Sourah Baqara

Станут ли талибы союзниками Израиля? @New Rush Word

Станут ли талибы союзниками Израиля? @New Rush Word

الاحسان\خطبة الجمعة \الشيخ ابراهيم صالح الحسيني

الاحسان\خطبة الجمعة \الشيخ ابراهيم صالح الحسيني

Польза от чтения книг | Хусейн Мержоев | Хутба 19.12.2025

Польза от чтения книг | Хусейн Мержоев | Хутба 19.12.2025

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Makari

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Makari

JNI Congratulates Shaykh Sharif Ibrahim Saleh on His Honorary Doctorate Award by ABU #jni_Nigeria

JNI Congratulates Shaykh Sharif Ibrahim Saleh on His Honorary Doctorate Award by ABU #jni_Nigeria

в чем секрет евреев

в чем секрет евреев

Цевехъанлъи ва жив веццизе вокьи . АЛИХАДЖИ АЛЬ-КИКУНИ

Цевехъанлъи ва жив веццизе вокьи . АЛИХАДЖИ АЛЬ-КИКУНИ

August 26, 2025

August 26, 2025

YADDA PROF. MAKARI YAYI FATA_FATA DA SHEIK JAFAR ADAM KANO.  Lallai Jiya ba yauba.

YADDA PROF. MAKARI YAYI FATA_FATA DA SHEIK JAFAR ADAM KANO. Lallai Jiya ba yauba.

ПОВЕРХНОСТНОЕ МЫШЛЕНИЕ, РАЗРУШАЮЩЕЕ УММУ | Шейх Мухаммад Муджир аль-Хатыб

ПОВЕРХНОСТНОЕ МЫШЛЕНИЕ, РАЗРУШАЮЩЕЕ УММУ | Шейх Мухаммад Муджир аль-Хатыб

© 2025 dtub. Все права защищены.

  • Контакты
  • О нас
  • Политика конфиденциальности

Контакты для правообладателей: [email protected]