Yadda Nijeriya za ta tunkari barazanar harin Amurka
Автор: TRT Afrika Hausa
Загружено: 2025-11-03
Просмотров: 26351
Babban labarin da yake ci gaba da daukar hankali shi ne matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai dauka kan Nijeriya, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai hari Nijeriya bayan da shugaban ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a kasar.
Trump ya bayar da umarnin ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео mp4
-
Информация по загрузке: