Ciwon hakori ne ya kai Janar Buhari London inda ajali ya riske shi-Sheikh Isa Ali Pantami
Автор: Nasiru Adamu El-hikaya
Загружено: 2025-08-10
Просмотров: 41
“Ina rubuta tarihi kan rayuwar shugaba Buhari” Inji Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami. A zantawa ta ta’aziyya da na yi ma sa kan rasuwar Janar Buhari bayan wani taro a Abuja, Sheikh Pantami ya ce faifan nan da ya zanta da marigayin a cikin aikin rubuta tarihin ne. Malamin ya tuno cewa ba a kawo tunanin rasuwar marigayi a lokacin da ya tafi London ba don a duba shi kan ciwon hakori; amma ajali ne ya zo da ke kan kowa. Sheikh Pantami wanda ya ce ya na da wasu faya-fayai na zantawa da marigayin da in Allah ya yarda zai fito da su, ya ce marigayin tamkar uba ne a gare shi. A nan Malamin ya kawo tarihin tun tashin marigayi a maraya ya shiga soja har ya yi shugaban kasa ya na matashi har zuwa rasuwar sa a shekaru 82. Ga zantawar
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео mp4
-
Информация по загрузке: