SHIGAR SANATA ALIYU MAGATAKARDA WAMAKKO A GARIN TAMBUWAL
Автор: 3STAR STUDIO
Загружено: 2020-08-26
Просмотров: 3074
GAISUWAR RASUWAR HAJIYA HAFSATU BELLO, ZAYYANU ALH. TSOHO DA SARKIN SHANU ALH. BELLO TAMBUWAL:
Duk a cikin garin Tambuwal, a yau Larba, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yakin Sokoto Kuma Marafan Hausa, ya ziyarci kanwurin Tambuwal a Gidan Marigayi Alh. Bello Sarkin shanu domin yiwa iyalai da Yan uwa gaisuwar wannan rashin da aka yi.
Sanata Wamakko ya Kuma yi irin wannan gaisuwar a Gidan Marigayi Zayyanu Alh tsoho Tambuwal Wanda ya rasu yana sati Daya da aka Daura Masa aure.
Haka Kuma , Sanata Wamakko ya Isar da irin wannan gaisuwar ta Rasuwar Hajiya Hafsatu Bello Tambuwal wacce Allah ya yiwa Rasuwa kwanan nan.
A duk inda Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ziyarta, ya roki Allah subhanahu wata'ala da ya yi gafara ga Marigayan ya baiwa iyalan su hakurin jure wannan rashin.
Sanata Wamakko ya bayyana wadannan rashe-rashen da cewa ba karamin Rashi ne ba, inda daga nan ya roki Allah subhanahu wata'ala da ya yi gafara ga resu Baki Daya mu kuwa ya kyautata tamu baya ga tasu.
Mallam Bashir Gidan Kanawa shi ne ya gudanar da addu'o'i na samun rahamar Allah zuwa ga ruhin Marigayan.
Sanata Wamakko tun da farin sai da ya sami tarbo na Musamman daga jagororin Jam'iyyar APC na karamar Hukumar Mulki ta Tambuwal kamar irin su Alh Abubakar Muhammad Babba Tambuwal, da sauran Manyam jigogin Jam'iyyar ta APC dake Tambuwal.
Sanata Wamakko haka kuma a duk inda ya je gaisuwar Yana samun rakiya da tarbo daga magoya bayan Jam'iyyar APC na yankin Tambuwal, maza da Mata da Matasa da dattijai domin Kara jaddada goyon bayan su ga tafiyar Mai girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto Shugaban Kwamitin tsaro na Majalisar dattawa ta Kasa.
A lokacin Ziyarar, Sanata Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko tun da farko har dawowa gida Sakkwato, yana tare da rakiyar Alh. Umaru Nagwari Tambuwal,tsoffin Manya Sakatarori Alh Bello Muhammad Sifawa, Alh Aminu Abdullahi Dodo Iyan Sokoto da Alh Sulaiman S Fulani Ahmadu.
Sauran sun hada da Sakataren Jam'iyyar APC na Jihar Sakkwato Alh Abubakar Muhammad Yabo, Ma'ajin Jam'iyyar APC,Alh Haruna S Gobir, kakakin Jam'iyyar APC,Alh Sambo Bello Danchadi, Uban Dawakin Gidan Bubu Alh Muhammadu Gidado da Barista Bello Muhammad Goronyo, Mai bada shawara Kan sha'anin Shari'a ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dai sauran su.
Hoto:Abdulrazak Umar.
Labari: Bashar Abubakar MC Sarkin Hausawan Sarkin Yamman Sokoto.
Larba 26/8/2020.
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео mp4
-
Информация по загрузке: